1 Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,
2 “Ɗan mutum, ka fuskanci wajen Ammonawa, ka yi annabci a kansu.
3 Ka faɗa musu su ji maganar Ubangiji Allah.” Ubangiji Allah ya ce, “Da yake kun ce, ‘Madalla,’ a lokacin da aka ƙazantar da Haikalina, da lokacin da ƙasar Isra'ila ta zama kufai, da lokacin da aka kai mutanen Yahuza bautar talala,
4 domin haka zan bashe ku abin mallaka ga mutanen gabas. Za su kafa alfarwansu a cikinku, su zauna tare da ku. Za su ci amfanin gonakinku, su sha madararku.
5 Zan mai da Rabba makiyayar raƙuma, in mai da biranen Ammonawa garken awaki da tumaki. Sa'an nan ku sani ni ne Ubangiji Allah.”
6 Gama Ubangiji Allah ya ce, “Da yake kun tafa hannuwanku, kun buga ƙafafunku, kuka yi murna don nuna dukan ƙiyayyarku da ƙasar Isra'ila,
7 domin haka zan miƙa hannuna gāba da ku, zan bashe ku, ku lalace a ƙasashe, zan hallaka ku. Sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji.”