1 A rana ta fari ga watan, a shekara ta goma sha ɗaya, sai kuma Ubangiji ya yi magana da ni ya ce,
2 “Ɗan mutum, da yake Taya ta yi magana a kan Urushalima ta ce, ‘Madalla, Urushalima ta rushe, ƙofa ta buɗu, yanzu zan wadata da yake ta zama kufai,’
3 domin haka ni, Ubangiji Allah na ce, ‘Ina gāba da ke, ke Taya, zan kawo al'ummai da yawa su yi gāba da ke, kamar yadda teku takan kawo raƙuman ruwa.
4 Za su hallaka garun Taya, su rurrushe hasumiyarta. Zan ƙan'kare ƙasarta, in maishe ta fā.