8 Zai kashe ya'yanki mata waɗanda suke a filin ƙasar da takobi. Zai kuma kewaye ki da garun yaƙi, ya gina miki mahaurai, sa'an nan zai rufe ki da garkuwoyi.
9 Zai rushe garunki da dundurusai, ya rushe hasumiyarki da gatura.
10 Saboda yawan dawakansa, ƙurar da za su tayar za ta rufe ki. Garunki kuma zai girgiza saboda motsin sojojin doki, da na ƙafafu kamar na keke, da na karusai sa'ad da ya shiga ƙofofinki, kamar yadda akan shiga birnin da garunsa ya rushe.
11 Kofatan dawakansa za su tattake dukan titunanki, zai kashe mutanenki da takobi. Manyan ginshiƙanki za su rushe.
12 Za su washe dukiyarki da kayan cinikinki. Za su kuma rurrushe garunki da kyawawan gidajenki. Za su kwashe duwatsu, da katakai, da tarkace, su zubar a cikin teku.
13 Zan sa a daina raira waƙoƙi da kaɗa garayu.
14 Zan maishe ki fā, wato wurin shanya taruna. Ba za a sāke gina ki ba, ni Ubangiji Allah na faɗa.”