19 Mutanen Dan, da Yawan, da ulu suka sayi kayanki, wato gyararren ƙarfe da kayan yaji.
20 Dedan ta sayi kayanki da kayan dawakai.
21 Mutanen Arabiya da shugabannin Kedar sun sayi kayanki da 'yan raguna, da raguna, da awaki.
22 'Yan kasuwar Sheba da Ra'ama sun sayi kayanki da kayan yaji mafi kyau iri iri, da duwatsu masu daraja iri iri, da zinariya.
23 Garuruwan Haran, da Kanne, da Aidan, da fataken Sheba, da Asshur, da Kilmad sun yi ciniki da ke.
24 Sun sayar miki da tufafi masu tsada, da na shuɗi, da masu ado, da darduma masu ƙyalƙyali da kirtani, da igiyoyi waɗanda aka tufka da kyau.
25 Jiragen ruwan Tarshish suna jigilar kayan cinikinki.Don haka kin bunƙasa,Kin ɗaukaka a tsakiyar tekuna.