5 Sun yi katakanki da itacen fir na Senir,Sun sari itacen al'ul daga Lebanon don su yi miki jigon jirgin ruwa.
6 Sun yi matuƙan jirgin ruwanki da katakon itacen oak na Bashan.Sun daɓe jirgin ruwanki da itacen kasharina na bakin tekun Kittim,Sa'an nan sun manne masa hauren giwa.
7 An yi filafilan jirgin ruwanki da lilin mai kyau, mai ado daga Masar,Don ya zama alama.An yi tutar jirgin ruwanki da shuɗi da shunayya na gaɓar tekun Elisha.
8 Mazaunan Sidon da Arwad su ne matuƙa,Masu hikima, waɗanda suke cikinki, su ne jagora.
9 Dattawan Gebal da masu hikimarta suna tare da ke,Suna tattoshe mahaɗan katakon jirginki,Dukan matuƙan jiragen ruwa sun zo wurinki don kasuwanci.
10 “ ‘Mutanen Farisa, da na Lud, da na Fut suna cikin sojojinki don su yi miki yaƙi. Sun rataya garkuwoyi, da kwalkwali a cikinki. Sun samo miki daraja.
11 Mutanen Arward sun kewaye kan garunki. Mutanen Gamad kuma suna tsaron hasumiyarki. Sun rataya garkuwoyinsu a jikin garunki. Sun ƙawata ki ƙwarai.