3 Lalle ka fi Daniyel hikima,Ba asirin da yake ɓoye a gare ka.
4 Ta wurin hikimarka da ganewarka ka samo wa kanka dukiya,Ka tattara zinariya da azurfa a baitulmalinka.
5 Saboda yawan hikimarka na yin kasuwanci, ka ƙara dukiyarka,Sai dukiyarka ta sa zuciyarka ta cika da alfarma.’
6 “Saboda haka Ubangiji Allah ya ce,‘Da yake ka aza kanka mai hikima ne kamar Allah,
7 Don haka zan tura baƙi a kanka,Waɗanda suka fi mugunta cikin sauran al'umma.Za su zare takubansu a kan kyakkyawar hikimarka,Za su ɓara darajarka.
8 Za su jefar da kai cikin rami,Za ka mutu kamar waɗanda suka mutu a tsakiyar teku.
9 Har yanzu za ka ce kai allah ne a gaban waɗanda suke ji maka rauni, Ko da yake kai mutum ne kawai, ba Allah ba?