2 “Ɗan mutum, ka fuskanci Fir'auna Sarkin Masar, ka yi annabci gāba da shi da dukan Masar.
3 Ka yi magana, ka ce, Ubangiji Allah ya ce,‘Ga shi, ina gāba da kai, kai Fir'auna Sarkin Masar,Babban mugun dabba wanda yake kwance a tsakiyar koguna,Wanda yake cewa, Kogin Nilu naka ne, kai ka yi shi.
4 Zan sa ƙugiyoyi a muƙamuƙanka,In kuma sa kifayen kogunanka su manne a ƙamborinka,Zan jawo ka daga cikin tsakiyar kogunanka,Da dukan kifayen kogunanka, waɗanda suka manne a ƙamborinka,
5 Zan yashe ka, kai da dukan kifayen kogunanka cikin jeji.Za ka fāɗi a fili, ba kuwa wanda zai ɗauke ka, ya binne ka.Zan sa ka zama abincin namomin jeji da tsuntsayen sararin sama.
6 A sa'an nan mazaunan Masar za su sani ni ne Ubangiji,Domin sun zama wa mutanenIsra'ila kamar sandan iwa.
7 Sa'ad da suka riƙe ka,Sai ka karye ka tsattsaga hannuwansu.Sa'ad da suka jingina da kai,Sai ka karye, har ka sa kwankwasonsu ya firgiza.
8 Saboda haka, ni Ubangiji Allah na ce zan jawo takobi a kanka, in kashe mutanenka, duk da dabbobi.