14 Zan sa Fatros ta zama kufai,Zan kunna wa Zowan wuta,Zan kuma shara'anta No.
15 Zan kwarara hasalata a kan Felusiyum,Wato kagarar Masar,Zan datse jama'ar No.
16 Zan kunna wa Masar wuta.Felusiyum za ta sha azaba mai tsanani,No kuwa za a tayar mata da hankali,Za a rurrushe garukanta.Za a tasar wa Memfis dukan yini.
17 Samarin Awen da na Fi-besetZa a kashe su da takobi,Matan kuma za su tafi bauta.
18 A Tafanes rana za ta yi duhu,Sa'ad da na karya mulkin ƙasar Masar,Ƙarfinta da take fariya da shi zai ƙare,Za a rufe ta da gizagizai.'Ya'yanta mata kuwa za a kai su bauta.
19 Ta haka zan hukunta Masar,Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji.”
20 A kan rana ta bakwai ga watan fari, a shekara ta goma sha ɗaya, sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,