1 A kan rana ta fari ga watan uku a shekara ta goma sha ɗaya, Ubangiji ya kuma yi magana da ni, ya ce,
2 “Ɗan mutum, ka ce wa Fir'auna, Sarkin Masar, da jama'arsa.‘Da wa za a kamanta girmanka?
3 Kana kama da Assuriya mai kama da itacen al'ul a Lebanon,Mai rassa masu kyau da inuwar kurmi,Mai tsayi ainun, kansa ya kai cikin gizagizai.
4 Ruwa ya sa ya yi girma,Danshi ya sa ya yi tsayi.Koguna sun gudu kewaye da wurin da aka shuka shi.Yana aikar da rafuffukansa zuwa dukan itatuwan kurmi.
5 Sai ya yi tsayi fiye da dukan itatuwan da suke a kurmi,Rassansa suka yi kauri, suka kuma yi tsayi,Saboda isasshen ruwa a lokacin tohonsa.
6 Dukan tsuntsayen sararin sama sun yi sheƙunansu a rassansa,Namomin jeji kuma suka haifi 'ya'yansu ƙarƙashin rassansa.Dukan al'ummai suka zauna ƙarƙashin inuwarsa.
7 Girmansa yana da kyau, haka kuma dogayen rassansa,Gama saiwoyinsa sun nutse can ƙasa har cikin ruwa.