3 Ubangiji Allah ya ce,‘Zan jefa taruna a kanka, a babban taron mutane,Zan jawo ka cikin taruna.
4 Zan jefar da kai a tudu,A fili zan jefa ka.Zan sa tsuntsayen sararin sama su ɗira a kanka,Zan ƙosar da namomin jeji na dukan duniya da namanka.
5 Zan watsa namanka a kan duwatsu,In cika kwaruruka da gawarka.
6 Zan watsar da jininka a ƙasa da tuddai,Magudanan ruwa za su cika da jininka.
7 Sa'ad da na shafe ka, zan rufe sammai,In sa taurarinsu su duhunta,Zan sa girgije ya rufe rana,Wata kuma ba zai haskaka ba.
8 Dukan haskokin sama zan sa su zama duhu a gare ka,In sa ƙasarka ta duhunta, ni Ubangiji Allah na faɗa.’
9 “Zukatan al'ummai da yawa za su ɓaci, sa'ad da na baza labarin halakarka a ƙasashen da ba ka sani ba.