1 Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,
2 “Ɗan mutum, ka yi annabci a kan makiyayan Isra'ila, ka ce musu, ‘Ku masu kiwon mutanen Isra'ila, ni Ubangiji Allah na ce, kaito, kaito, ku masu kiwon mutanen Isra'ila, kuna kiwon kanku kawai! Ashe, ba makiyaya ne suke kiwon tumaki ba?
3 Kuna cin kitsensu, kuna yi wa kanku tufafi da gashinsu, kukan yanka turkakkun, amma ba ku yi kiwon tumakin ba.
4 Ba ku ƙarfafa marasa ƙarfi ba, ba ku warkar da marasa lafiya ba, ba ku ɗora karayyu ba, waɗanda kuma suka yi makuwa ba ku komar da su ba, waɗanda suka ɓace ba ku nemo su ba, amma kuka mallake su ƙarfi da yaji.
5 Sai suka warwatsu saboda rashin makiyayin kirki, suka zama abincin namomin jeji.