2 “Ɗan mutum, ka fuskanci Dutsen Seyir, ka yi annabci a kansa.
3 Ka faɗa masa, ni Ubangiji Allah na ce,Ga shi, ina gāba da shi, wato Dutsen Seyir.Zan miƙa hannuna gāba da shi,Zan maishe shi kufai, in lalatar da shi.
4 Zan lalatar da biranensa,In maishe su kufai marar amfani,Sa'an nan zai sani ni ne Ubangiji.
5 “Saboda ya riƙe ƙiyayya din din din, ya ba da mutanen Isra'ila domin a kashe su da takobi a lokacin masifarsu, da lokacin da adadin horonsu ya cika,
6 don haka, ni Ubangiji na ce, hakika zan sa a zub da jininsa. Mai zub da jini zai fafare shi, da yake shi ma ya zub da jini, domin haka mai zub da jini zai fafare shi.
7 Zan mai da Dutsen Seyir kufai marar amfani. Zan kashe duk mai shiga ko mai fita a cikinsa.
8 Zan cika duwatsunsa da gawawwaki. Waɗanda za a kashe da takobi za su faɗi a kan tuddansa, da cikin kwarurukansa, da cikin dukan kwazazzabansa.