1 “Kai ɗan mutum, ka yi annabci a kan duwatsun Isra'ila, ka ce, ‘Ya duwatsun Isra'ila, ku ji maganar Ubangiji.’
2 Ubangiji Allah ya ce, da yake maƙiya suna cewa, ‘Madalla, tsofaffin tuddai sun zama mallakarmu yanzu,’
3 sai ka yi annabci ka ce, ni Ubangiji Allah na ce, ‘Da yake sun maishe ku kufai marar amfani, sun kuma murƙushe ku ta kowace fuska, har kun zama abin mallakar sauran al'umma, kun zama abin magana da abin tsegumi ga mutane.
4 Domin haka, ku duwatsun Isra'ila, sai ku ji maganar Ubangiji Allah. Ni Ubangiji Allah, na ce wa duwatsu, da tuddai, da kwazazzabai, da kwaruruka, da kufai, da yasaassun birane waɗanda suka zama ganima da abin ba'a ga al'umman da suke kewaye,
5 ni, Ubangiji Allah, ina yin magana da zafin kishina gāba da sauran al'umma, da dukan Edom, gama da farin ciki da raini suka mallaki ƙasata, suka washe ta.’