21 sai ka faɗa musu, cewa ni Ubangiji Allah na ce, zan komo da jama'ar Isra'ila daga wurin al'ummai inda suka warwatsu, zan tattaro su daga ko'ina, in maido su ƙasarsu.
22 Zan maishe su al'umma guda a ƙasar Isra'ila. Sarki ɗaya zai sarauce su duka, ba za su ƙara zama al'umma biyu ba, ba kuwa za su ƙara zama masarauta biyu ba.
23 Ba za su ƙara ƙazantar da kansu da gumaka da abubuwan banƙyama da kowane irin laifi ba. Zan komo da su daga riddar da suka yi, in tsarkake su. Za su zama jama'ata, ni kuma zan zama Allahnsu.
24 Bawana Dawuda zai sarauce su. Dukansu za su sami shugaba guda. Za su bi ka'idodina su kiyaye dokokina.
25 Za su zauna a ƙasar da kakanninsu suka zauna, wadda na ba bawana Yakubu. Su da 'ya'yansu da jikokin 'ya'yansu za su zauna a can har abada. Bawana Dawuda kuwa zai sarauce su har abada.
26 Zan ƙulla dawwamammen alkawarin salama da su. Zan sa musu albarka, in yawaita su. Zan kafa Haikalina a tsakiyarsu har abada.
27 Wurin Zamana zai kasance a tsakiyarsu, zan zama Allahnsu, su kuma za su zama mutanena.