23 Ba za su ƙara ƙazantar da kansu da gumaka da abubuwan banƙyama da kowane irin laifi ba. Zan komo da su daga riddar da suka yi, in tsarkake su. Za su zama jama'ata, ni kuma zan zama Allahnsu.
24 Bawana Dawuda zai sarauce su. Dukansu za su sami shugaba guda. Za su bi ka'idodina su kiyaye dokokina.
25 Za su zauna a ƙasar da kakanninsu suka zauna, wadda na ba bawana Yakubu. Su da 'ya'yansu da jikokin 'ya'yansu za su zauna a can har abada. Bawana Dawuda kuwa zai sarauce su har abada.
26 Zan ƙulla dawwamammen alkawarin salama da su. Zan sa musu albarka, in yawaita su. Zan kafa Haikalina a tsakiyarsu har abada.
27 Wurin Zamana zai kasance a tsakiyarsu, zan zama Allahnsu, su kuma za su zama mutanena.
28 Sa'an nan al'ummai za su sani, ni ne na tsarkake Isra'ila sa'ad da na kafa Haikalina a tsakiyarsu har abada.”