8 Da na duba, sai ga jijiyoyi a kansu, nama kuma ya baibaye su, sa'an nan fata ta rufe su, amma ba numfashi a cikinsu.
9 Sa'an nan Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum, ka yi annabci a kan iska, ka ce mata, ni Ubangiji Allah na ce ta zo daga kusurwa huɗu, ta hura a kan waɗannan matattu domin su rayu.”
10 Na kuwa yi annabci kamar yadda aka umarce ni, sai numfashi ya shiga cikinsu, suka rayu, suka tashi, suka tsaya da ƙafafunsu. Sun zama babbar runduna ƙwarai.
11 Sa'an nan Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum waɗannan ƙasusuwa su ne mutanen Isra'ila duka. Ga shi, suna cewa, ‘Ƙasusuwa sun bushe, zuciyarmu kuwa ta karai, an share mu ƙaƙaf.’
12 “Domin haka ka yi annabci ka ce musu, ni Ubangiji Allah na ce zan buɗe kaburburansu, in tashe su daga cikin kaburburansu. Zan kuma komar da su gida zuwa ƙasar Isra'ila.
13 Mutanena za su sani ni ne Ubangiji sa'ad da na buɗe kaburburansu na tashe su daga cikinsu.
14 Zan sa Ruhuna a cikinsu za su kuwa rayu. Zan sa su a ƙasarsu sa'an nan za su sani ni Ubangiji na faɗa, na kuwa aikata.”