1 “Kai ɗan mutum, sai ka faɗa wa Gog shugaban Rosh, da Meshek, da Tubal cewa, ‘Ni Ubangiji Allah ina gāba da kai.
2 Zan juya ka in sa ka gaba in tashi daga ƙurewar arewa, in kawo ka don ka fāɗa wa duwatsun Isra'ila.
3 Sa'an nan zan karya bakan da yake a hannun hagunka, in sa kiban da suke a hannun damanka su fāɗi.
4 Za ka fāɗi matacce a kan duwatsun Isra'ila, kai da dukan rundunanka, da jama'ar da suke tare da kai. Zan ba da gawawwakinka ga tsuntsaye da dabbobi masu cin nama.
5 Za ka mutu a filin saura, gama haka ni Ubangiji Allah na faɗa.’