17 “Ni Ubangiji Allah na ce, kai ɗan mutum, sai ka gayyato kowane irin tsuntsu da dukan bisashe daga ko'ina, su zo idi wanda nake shirya musu a duwatsun Isra'ila. Za su ci nama su kuma sha jini.
18 Za su ci naman mutane masu iko, su sha jinin shugabannin duniya, waɗanda aka kashe kamar yadda ake yanka raguna, da 'yan tumaki, da awaki, da bijimai, da dukan turkakkun Bashan.
19 Za su ci kitse, har su gundura, su sha jini kuma, har su bugu a idin da nake shirya musu.
20 Za a ƙosar da su da naman dawakai, da na mahayansu da na mutane masu iko, da na dukan mayaƙa, ni Ubangiji na faɗa.”
21 “Zan nuna ɗaukakata a cikin al'ummai, dukan al'ummai kuwa za su ga hukuncin da na yi da ikon da na nuna kansu.
22 Tun daga wannan rana har zuwa gaba, jama'ar Isra'ila za su sani, ni ne Ubangiji Allahnsu.
23 Al'ummai kuma za su sani an kai jama'ar Isra'ila zaman bautar talala saboda muguntarsu, domin sun yi mini ha'inci, ni kuwa na kawar da fuskata daga gare su, na bashe su a hannun abokan gābansu, suka ci su da yaƙi.