7 Zan sanar da sunana mai tsarki a tsakiyar jama'ata, wato Isra'ila, ba zan ƙara bari a ɓata sunana mai tsarki ba, al'ummai kuwa za su sani ni ne Ubangiji Mai Tsarki a cikin Isra'ila.
8 “Ga shi, ranar da na ambata tana zuwa, hakika kuwa tana zuwa, ni Ubangiji Allah na faɗa.
9 Sa'an nan su mazaunan biranen Isra'ila za su tattara makaman mutane, wato garkuwoyi, da bakuna, da kibau da kulake, da māsu, su yi ta hura wuta da su, har ya kai shekara bakwai.
10 Ba za su yi wahalar zuwa jeji don nemo itacen wuta ba, gama za su yi ta hura wuta da makaman. Za su washe waɗanda suka washe su a dā, ni Ubangiji na faɗa.
11 “A wannan rana zan ba Gog makabarta a Isra'ila, a kwarin matafiya a gabashin teku. Makabartar za ta kashe hanyar matafiya, gama a can za a binne Gog da dukan rundunar da take tare da shi. Za a kira wurin Hamongog, wato Kwarin Rundunar Gog.
12 Jama'ar Isra'ila za su yi wata bakwai suna binne su don su tsabtace ƙasar.
13 Dukan jama'ar ƙasar za su yi aikin binnewar, zai zama daraja a gare su a ranar da zan bayyana ɗaukakata, ni Ubangiji Allah na faɗa.