1 Bayan haka kuma sai ya kai ni ƙofar da take fuskantar gabas.
2 Sai ga zatin Allah na Isra'ila yana tahowa daga gabas. Muryar Allah ta yi amo kamar rurin teku. Duniya kuwa ta haskaka da zatinsa.
3 Wahayin da na gani ya yi kama da wahayin da na gani lokacin da ya hallaka birnin, kamar kuma wanda na gani a bakin kogin Kebar. Sai na fāɗi rubda ciki.
4 Zatin Ubangiji ya shiga Haikalin ta ƙofar gabas.
5 Ruhu kuwa ya ɗaga ni, ya kai ni a farfajiya ta can ciki, sai ga zatin Ubangiji ya cika Haikali.