17 Sa'ad da suka shiga ƙofofin fili na can ciki, sai su sa rigunan lilin, kada su sa abin da aka yi shi da ulu, sa'ad da suke hidima a ƙofofin fili na can ciki, da cikin Haikalin.
18 Za su naɗa rawunan lilin, su sa wandunan lilin. Kada su sa abin da zai sa su yi zuffa.
19 Sa'ad da suka fita zuwa filin da yake waje, wurin mutane, sai su tuɓe tufafin da suka yi hidima da su, su ajiye su a tsarkakakkun ɗakuna, sa'an nan su sa waɗansu tufafi domin kada su tsarkake mutane da tsarkakakkun tufafinsu.
20 “Ba za su aske kansu ba, ba kuma za su bar zankayensu su yi tsayi ba, sai su sausaye gashin kansu.
21 Kada firist ya sha ruwan inabi sa'ad da zai shiga fili na can ciki.
22 Ba za su auri gwauruwa ba, wato wadda mijinta ya rasu, ko sakakkiya, sai budurwa daga zuriyar Isra'ila, ko kuwa matar firist wanda ya rasu.
23 “Za su koya wa jama'ata bambancin halal da haram, su kuma nuna musu yadda za su rarrabe tsakanin tsattsarka da marar tsarki.