1 “Sa'ad da kuka rarraba ƙasar gādo, sai ku keɓe wa Ubangiji wani wuri domin ya zama yanki mai tsarki, tsawonsa zai zama kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], faɗinsa kuwa kamu dubu goma [10,000]. Dukan yankin zai zama wuri mai tsarki.
2 Daga cikin wannan, murabba'i mai tsawo kamu ɗari biyar, da faɗi ɗari biyar, zai zama wuri mai tsarki, fili kuma mai kamu hamsin zai kewaye wurin nan mai tsarki.
3 A cikin yanki mai tsarki za ka auna tsawo kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], da faɗi kamu dubu goma [10,000], inda Wuri Mafi Tsarki zai kasance.
4 Wannan yanki shi ne zai zama wuri mai tsarki na ƙasar. Zai zama na firistoci waɗanda suke hidima a cikin Haikali, waɗanda suke kusatar Ubangiji don su yi masa hidima. Wurin zai zama wurin gina gidajensu da kuma wuri mai tsarki domin Haikalin.
5 Wani sashi kuma mai tsawo kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], da faɗi kamu dubu goma [10,000], zai zama na Lawiyawa masu hidima cikin Haikalin, zai zama wurin da za su mallaka, su zauna a ciki.
6 Za ku tsaga wa birnin hurumi mai fāɗi kamu dubu biyar, da tsawo kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], rabe da yankin nan mai tsarki. Hurumin zai zama na mutanen Isra'ila duka.”