16 da Hamat, da Berota, da Sibrayim, wadda take a iyakar tsakanin Dimashƙu da Hamat, har zuwa Hazer-hattikon wadda take iyakar Hauran.
17 Iyakar za ta bi daga teku zuwa Hazar-enan wadda take iyakar Dimashƙu. Iyakar Hamat tana wajen arewa. Wannan ita ce iyakar a wajen arewa.
18 “A wajen gabas, iyakar za ta kama daga Hazar-enan tsakanin Hauran da Dimashƙu, ta bi ta Urdun tsakanin Gileyad da ƙasar Isra'ila zuwa tekun gabas har zuwa Tamar. Wannan ita ce iyakar a wajen gabas.
19 “A wajen kudu, iyakar za ta kama daga Tamar har zuwa ruwan Meribakadesh, ta bi ta rafin Masar zuwa Bahar Rum. Wannan ita ce iyakar a wajen kudu.
20 “A wajen yamma, Bahar Rum shi ne iyakar zuwa ƙofar Hamat. Wannan ita ce iyakar a wajen yamma.
21 “Za ku kuwa raba ƙasar a tsakaninku bisa ga kabilan Isra'ila.
22 Za ku raba ƙasar gādo a tsakaninku da baƙin da suke zaune tare da ku, waɗanda suka haifi 'ya'ya a cikinku. Za su zama kamar 'ya'yan Isra'ila haifaffu na gida. Za a ba su gādo tare da kabilan Isra'ila,