23 “Sauran kabilan kuwa za su samu. Biliyaminu zai sami yankinsa daga gabas zuwa yamma.
24 Yankin Saminu yana kusa da yankin Biliyaminu daga gabas zuwa yamma.
25 Yankin Issaka yana kusa da yankin Saminu daga gabas zuwa yamma.
26 Yankin Zabaluna yana kusa da yankin Issaka daga gabas zuwa yamma.
27 Yankin Gad yana kusa da yankin Zabaluna daga gabas zuwa yamma.
28 “Kusa da yankin Gad zuwa kudu, iyakar za ta bi ta Tamar zuwa ruwan Meriba-kadesh, sa'an nan ta bi rafin Masar zuwa Bahar Rum.”
29 Ubangiji ya ce, “Wannan ita ce hanyar da za ku raba gādo tsakanin kabilan Isra'ila. Waɗannan kuwa su ne yankunansu, ni Ubangiji Allah na faɗa.”