5 Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ɗaga idanunka, ka duba wajen arewa.” Na kuwa ɗaga idanuna wajen arewa, na kuma ga siffa ta tsokano kishi a mashigin ƙofar bagade na wajen arewa.
6 Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ka ga abin da suke yi, abubuwa masu banƙyama da mutanen Isra'ila suke yi a nan don su kore ni nesa da Haikalina? Ai, za ka ga abubuwa masu banƙyama da suka fi haka.”
7 Ya kuma kai ni ƙofar shirayi. Sa'ad da na duba, sai ga wani rami a bangon.
8 Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka haƙa bangon.” Da na haƙa bangon, sai ga ƙofa.
9 Ya ce, mini, “Ka shiga ka ga abubuwan banƙyama da suke aikatawa a nan.”
10 Da na shiga, sai na ga zānen siffofin kowane irin abu mai rarrafe, da haramtattun dabbobi, da dukan gumakan mutanen Isra'ila kewaye da bangon.
11 Dattawan Isra'ila saba'in suna tsaye a gabansu. Yazaniya ɗan Shafan yana tsaye tare da su. Kowa yana riƙe da farantin ƙona turare. Hayaƙin turaren ya tunnuƙe zuwa sama.