8 Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka haƙa bangon.” Da na haƙa bangon, sai ga ƙofa.
9 Ya ce, mini, “Ka shiga ka ga abubuwan banƙyama da suke aikatawa a nan.”
10 Da na shiga, sai na ga zānen siffofin kowane irin abu mai rarrafe, da haramtattun dabbobi, da dukan gumakan mutanen Isra'ila kewaye da bangon.
11 Dattawan Isra'ila saba'in suna tsaye a gabansu. Yazaniya ɗan Shafan yana tsaye tare da su. Kowa yana riƙe da farantin ƙona turare. Hayaƙin turaren ya tunnuƙe zuwa sama.
12 Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum ko ka ga abin da dattawan Isra'ilawa suke yi a cikin duhu? Kowa yana cikin ɗakin zānannun siffofin gumaka, sukan ce, ‘Allah ba ya ganinmu. Ubangiji ya rabu da ƙasan nan.”’
13 Ya kuma ce mini, “Har yanzu dai za ka ga abubuwa masu banƙyama da suka fi haka waɗanda suke aikatawa.”
14 Sai ya kai ni a bakin ƙofar arewa ta Haikalin Ubangiji, ga kuwa mata a zaune suna kuka domin gunkin nan, Tammuz.