11 Sa'ad da yake gab da shiga Masar, ya ce wa matarsa, Saraya, “Na sani ke kyakkyawar mace ce,
12 lokacin da Masarawa suka gan ki za su ce, ‘Wannan matarsa ce,’ za su kashe ni, amma za su bar ki da rai.
13 Ki ce ke 'yar'uwata ce, domin dalilinki kome sai ya tafi mini daidai a kuma bar ni da raina.”
14 Sa'ad da Abram ya shiga Masar sai Masarawa suka ga matar kyakkyawa ce ƙwarai.
15 Da fādawan Fir'auna suka gan ta, sai suka yabe ta a gaban Fir'auna. Aka ɗauke ta aka kai ta gidan Fir'auna.
16 Saboda ita Fir'auna ya yi wa Abram alheri. Abram yana da tumaki, da takarkarai, da jakai maza, da barori mata da maza, da jakai mata, da raƙuma.
17 Sai Ubangiji ya wahalar da Fir'auna da gidansa da manya manyan annobai saboda matar Abram, Saraya.