9 Mala'ikan Ubangiji ya ce mata, “Koma wurin uwargijiyarki, ki yi mata ladabi.”
10 Mala'ikan Ubangiji kuma ya ce mata, “Zan riɓaɓɓanya zuriyarki ainun har da ba za a iya lasafta su ba saboda yawansu.”
11 Mala'ikan Ubangiji kuma ya ƙara ce mata, “Ga shi, kina da ciki, za ki haifi ɗa, za ki kira sunansa Isma'ilu, domin Ubangiji ya lura da wahalarki.
12 Zai zama mutum ne mai halin jakin jeji, hannunsa zai yi gāba da kowane mutum, hannun kowane mutum kuma zai yi gāba da shi. Zai yi zaman magabtaka tsakaninsa da 'yan'uwansa duka.”
13 Sai ta kira sunan Ubangiji wanda ya yi magana da ita, “Kai Allah ne mai gani,” gama ta ce, “Ni! Har na iya ganin Allah in rayu?”
14 Domin haka aka kira sunan rijiyar, Biyer-lahai-royi, tana nan tsakanin Kadesh da Bered.
15 Hajaratu ta haifa wa Abram ɗa, Abram kuwa ya sa wa ɗa da Hajaratu ta haifa suna, Isma'ilu.