13 Duka biyu, da wanda aka haifa daga gidanka, da wanda ka saya da kuɗi, za a yi musu kaciya. Da haka alkawarina zai kasance cikin jikinku, madawwamin alkawari ke nan.
14 Kowane ɗa namiji da bai yi kaciya ba, wato wanda bai yi kaciyar loɓarsa ba, za a fitar da shi daga jama'arsa, don ya ta da alkawarina.”
15 Allah ya ce wa Ibrahim, “Ga zancen matarka Saraya, ba za ka kira sunanta Saraya ba, amma Saratu ne sunanta.
16 Zan sa mata albarka, banda haka kuma zan ba ka ɗa ta wurinta, zan sa mata albarka, za ta kuwa zama mahaifiyar al'ummai, sarakunan jama'a za su fito daga gare ta.”
17 Sai Ibrahim ya yi ruku'u, ya yi dariya a zuciyarsa, ya ce wa kansa, “Za a haifa wa mai shekara ɗari ɗa? Zai yiwu Saratu mai shekara tasa'in ta haifi ɗa?”
18 Sai Ibrahim ya ce wa Allah, “Da ma dai a bar Isma'ilu kawai ya rayu a gabanka.”
19 Allah ya ce, “A'a, matarka Saratu ita ce za ta haifa maka ɗa, za ka raɗa masa suna Ishaku. A gare shi zan tsai da alkawarina madawwami, da kuma ga zuriyarsa a bayansa.