22 Sa'an nan mutanen suka juya daga nan, suka nufi Saduma, amma Ibrahim ya tsaya a gaban Ubangiji.
23 Sai Ibrahim ya matso kusa, ya ce, “Ashe, za ka hallaka adali tare da mugun?
24 Da a ce, akwai masu adalci hamsin cikin birnin, za ka hallaka wurin, ba za ka yafe su saboda masu adalcin nan hamsin waɗanda suke cikinsa ba?
25 Wannan ya yi nesa da kai, da ka aikata irin haka, wato da za ka aza mai adalci daidai yake da mugu! Wannan ya yi nesa da kai! Mahukuncin dukan duniya ba zai yi adalci ba?”
26 Sai Ubangiji ya ce, “In na sami adalai hamsin a cikin birnin Saduma, zan yafe wa dukan wurin sabili da su.”
27 Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga shi, na jawo wa kaina in yi magana da Ubangiji, ni da nake ba kome ba ne, amma turɓaya ne da toka.
28 Da a ce za a rasa biyar daga cikin adalai hamsin ɗin, za ka hallaka birnin duka saboda rashin biyar ɗin?”Sai ya ce, “Ba zan hallaka shi ba in na sami arba'in da biyar a wurin.”