31 Ya ce masa, “Shigo, ya mai albarka na Ubangiji, don me kake tsaye a waje? Gama na shirya gida da wuri domin raƙuma.”
32 Mutumin ya shiga gidan, Laban kuwa ya sauke raƙuman, ya ba shi baro da harawa domin raƙuma, da ruwa ya wanke ƙafafunsa da ƙafafun waɗanda suke tare da shi.
33 Aka sa abinci a gabansa domin ya ci, amma ya ce, “Ba zan ci ba, sai na faɗi abin da yake tafe da ni.”Laban ya ce, “Faɗi maganarka.”
34 Ya ce, “Ni baran Ibrahim ne.
35 Ubangiji ya sa wa maigidana albarka ƙwarai, ya kuwa zama babba, ya ba shi garkunan tumaki da na shanu, da azurfa da zinariya, da barori mata da maza, da raƙuma da jakai.
36 Saratu ta haifa wa maigidana ɗa cikin tsufanta, a gare shi kuma ya ba da dukan abin da yake da shi.
37 Maigidana ya rantsar da ni da cewa, ‘Ba za ka auro wa ɗana mace daga cikin 'ya'yan Kan'aniyawa waɗanda nake zaune a ƙasarsu ba,