22 Saboda haka Yakubu ya matsa kusa da Ishaku mahaifinsa, sai ya lallaluba shi, ya ce, “Murya, muryar Yakubu ce, amma hannuwa, hannuwan Isuwa ne.”
23 Amma bai gane shi ba, gama hannuwansa gargasa ne kamar hannuwan ɗan'uwansa Isuwa, saboda haka ya sa masa albarka.
24 Ya ce, “Hakika, kai ne ɗana Isuwa?”Ya amsa, “Ni ne.”
25 Ya ce, “Kawo mini naman da ka harbo, in ci in sa maka albarka.” Sai ya kawo masa, ya kuwa ci, ya kawo masa ruwan inabi, ya sha.
26 Mahaifinsa Ishaku kuwa ya ce masa, “Zo kusa ka sumbace ni, ɗana.”
27 Don haka ya zo kusa ya sumbace shi. Ishaku ya sansana rigunansa, ya sa masa albarka, ya ce,“Duba, ƙanshin ɗanaYana kama da ƙanshin jejiWanda Ubangiji ya sa wa albarka!
28 Allah ya ba ka daga cikin raɓarsama,Daga cikin ni'imar ƙasa,Da hatsi a yalwace da ruwan inabi.