8 Yanzu fa, ɗana, ka biye wa maganata yadda zan umarce ka.
9 Je ka garke, ka kamo 'yan awaki biyu kyawawa, domin in shirya abinci mai daɗi da su domin mahaifinka, irin wanda yake so.
10 Kai kuwa ka kai wa mahaifinka, ya ci, domin ya sa maka albarka kafin ya rasu.”
11 Amma Yakubu ya ce wa Rifkatu mahaifiyarsa, “Ga shi fa, ɗan'uwana Isuwa gargasa ne, ni kuwa mai sulɓi ne.
12 Watakila, baba zai lallaluba ni, zai kuwa ce, ruɗinsa nake yi, in kuwa jawo wa kaina la'ana maimakon albarka.”
13 Sai mahaifiyarsa ta ce masa, “La'anarka ta faɗo bisa kaina, ɗana. Kai dai ka yi biyayya da maganata. Je ka, ka kamo mini.”
14 Ya tafi ya kamo su, ya kawo su ga mahaifiyarsa, mahaifiyarsa kuwa ta shirya abinci mai daɗi irin wanda mahaifinsa yake so.