8 sai Isuwa ya gane 'yan matan Kan'aniyawa ba su gamshi Ishaku mahaifinsa ba.
9 Saboda haka Isuwa ya tafi wurin Isma'ilu ya auro Mahalat 'yar'uwar Nebayot, 'yar Isma'ilu ɗan Ibrahim, banda matan da yake da su.
10 Yakubu ya bar Biyer-sheba ya kama hanya zuwa Haran.
11 Da ya isa wani wuri, sai ya kwana can a wannan dare, don rana ta riga ta faɗi. Ya ɗauki ɗaya daga cikin duwatsun da suke wurin, ya yi matashin kai da shi, ya kwanta, ya yi barci.
12 Ya yi mafarki, ga wani tsani tsaye daga ƙasa, kansa ya kai sama, sai ga mala'ikun Allah suna hawa da sauka ta kansa!
13 Ga shi kuwa, Ubangiji na tsaye a kansa yana cewa, “Ni ne Ubangiji, Allah na Ibrahim, mahaifinka, da Ishaku, ƙasar da kake kwance a kai, zan ba ka ita da zuriyarka.
14 Zuriyarka kuwa za su zama kamar turɓayar ƙasa, za su kuma bazu zuwa gabas da yamma, kudu da arewa. Ta wurinka da zuriyarka, iyalan duniya duka za su sami albarka.