6 Matar ta ga yadda itacen yana da kyau, 'ya'yansa kuma kyawawa, abin sha'awa ne kuma ga ido, abin marmari ne domin ba da hikima, ta tsinka daga 'ya'yansa, ta kuwa ci, ta kuma bai wa mijinta waɗansu, shi kuma ya ci.
7 Sai dukansu biyu idanunsu suka buɗe, sa'an nan suka gane tsirara suke, sai suka samo ganyayen ɓaure suka ɗinɗinka suka yi wa kansu sutura.
8 Da suka ji motsin Allah yana yawo a gonar da sanyin la'asariya, sai mutumin da matarsa suka ɓuya wa Ubangiji Allah cikin itatuwan gonar.
9 Amma Ubangiji Allah ya kira mutumin, ya ce, “Ina kake?”
10 Sai ya ce, “Na ji motsinka cikin gonar, na kuwa ji tsoro, domin tsirara nake, na kuwa ɓoye kaina.”
11 Ya ce, “Wa ya faɗa maka tsirara kake? Ko ka ci daga cikin itacen da na ce kada ka ci ne?”
12 Mutumin ya ce, “Matan nan da ka ba ni, ita ce ta ba ni 'ya'yan itacen, na kuwa ci.”