51 Sai Laban ya ce wa Yakubu, “Dubi wannan tsibi da al'amudi, wanda na kafa tsakanina da kai.
52 Wannan tsibi, shaida ce, al'amudin kuma shaida ce ba zan zarce wannan tsibi zuwa wurinka ba, kai kuma ba za ka zarce wannan tsibi da wannan al'amudi zuwa wurina don cutarwa ba.
53 Allah na Ibrahim da Nahor, Allah na mahaifinsu, ya shara'anta tsakaninmu.” Saboda haka Yakubu ya rantse da martabar mahaifinsa Ishaku.
54 Yakubu kuwa ya miƙa hadaya a bisa dutsen, ya kirawo iyalinsa su ci abinci, suka kuwa ci abinci suka zauna dukan dare a bisa dutsen.
55 Da sassafe, Laban ya tashi ya sumbaci jikokinsa, da 'ya'yansa mata, ya sa musu albarka. Sa'an nan ya tashi ya koma gida.