7 Yakubu fa ya tsorata ƙwarai, ya damu, sai ya karkasa mutanen da suke tare da shi, da garkunan tumaki da awaki, da na shanu, da raƙuma cikin ƙungiya biyu,
8 yana tunani cewa, “In Isuwa ya zo ya hallaka ƙungiya guda, ƙungiyar da ta ragu sai ta tsira.”
9 Sai Yakubu ya ce, “Ya Allah na kakana Ibrahim, da mahaifina Ishaku, Ubangiji, wanda ka ce mini, ‘Koma ƙasarka zuwa wurin danginka, zan kuwa yi maka alheri,’
10 ban cancanci ayyukanka na ƙauna da irin amincin da ka gwada wa baranka ba, gama da sandana kaɗai na haye Kogin Urdun, ga shi yanzu kuwa na zama ƙungiya biyu.
11 Ka cece ni ina roƙonka daga hannun ɗan'uwana, wato daga hannun Isuwa, gama ina jin tsoronsa, kada ya zo ya karkashe mu duka, 'ya'ya da iyaye.
12 Gama ka riga ka ce, ‘Zan yi maka alheri, in kuma sa zuriyarka su yi yawa kamar yashin teku, waɗanda ba su lasaftuwa saboda yawansu.’ ”
13 Ya yi zango a nan a wannan dare, ya kuwa bai wa ɗan'uwansa Isuwa kyauta daga cikin abin da yake da shi,