11 Allah ya ce masa, “Ni ne Allah Maɗaukaki, ka hayayyafa ka riɓaɓɓanya, al'umma da tattaruwar al'ummai za su bumbunto daga gare ka, sarakuna kuma za su fito daga cikinka.
12 Na ba ka ƙasar da na ba Ibrahim da Ishaku, zan kuma ba da ita ga zuriyarka a bayanka.”
13 Sa'an nan Allah ya tashi Sama ya bar shi a wurin da ya yi masa magana.
14 Sai Yakubu ya kafa al'amudin dutse a inda Allah ya yi masa magana, ya zuba masa sadaka ta sha, ya kuma zuba mai a bisansa.
15 Yakubu ya kira sunan wurin da Allah ya yi magana da shi, Betel.
16 Da suka tashi daga Betel, tun suna da 'yar rata da Efrata, sai lokaci ya yi da Rahila za ta haihu, amma ta sha wahala kafin ta haihu.
17 Sa'ad da take cikin naƙudarta, sai ungozoma ta ce mata, “Kada ki ji tsoro, gama yanzu kin sami wani ɗa.”