10 Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Isuwa, maza, wato Elifaz ɗan Ada matar Isuwa, Reyuwel ɗan Basemat matar Isuwa.
11 'Ya'yan Elifaz su ne Teman, da Omar, da Zeho, da Gatam, da Kenaz.
12 Timna kuwa ƙwarƙwarar Elifaz ɗan Isuwa ce, ta haifa wa Elifaz Amalek. Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Ada, matar Isuwa.
13 Waɗannan su ne 'ya'yan Reyuwel, maza, Nahat, da Zera, da Shamma, da Mizza. Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Basemat, matar Isuwa.
14 Waɗannan su ne 'ya'yan Oholibama matar Isuwa 'yar Ana ɗan Zibeyon. Ta haifi wa Isuwa Yewush, da Yalam, da Kora.
15 Waɗannan su ne shugabanni na zuriyar Isuwa. Ga 'ya'yan Elifaz, maza, ɗan farin Isuwa, shugaba Teman, da Omar, da Zeho, da Kenaz,
16 da Kora, da Gatam, da Amalek, su ne shugabannin Elifaz cikin ƙasar Edom, su ne 'ya'yan Ada.