16 da Kora, da Gatam, da Amalek, su ne shugabannin Elifaz cikin ƙasar Edom, su ne 'ya'yan Ada.
17 Waɗannan su ne 'ya'yan Reyuwel, maza, ɗan Isuwa. Shugaba Nahat, da Zera, da Shamma, da Mizza, waɗannan su ne shugabannin Reyuwel na cikin ƙasar Edom, su ne 'ya'ya maza na Basemat, matar Isuwa.
18 Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Oholibama matar Isuwa, shugaba Yewush, da Yalam, da Kora, waɗannan su ne shugabanni waɗanda Oholibama matar Isuwa, 'yar Ana ta haifa.
19 Waɗannan su ne 'ya'yan Isuwa, maza, wato Edom, da shugabanninsu.
20 Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Seyir Bahore, mazaunan ƙasar Lotan, da Shobal, da Zibeyon, da Ana,
21 da Dishon, da Ezer, da Dishan. Waɗannan su ne shugabannin Horiyawa, 'ya'yan Seyir, maza, a ƙasar Edom.
22 'Ya'yan Lotan, maza, su ne Hori da Hemam, 'yar'uwarsa Timna ce.