37 Fir'auna da fādawansa duka sun yarda da wannan shawara.
38 Sai Fir'auna ya ce wa fādawansa, “Mā iya samun mutum irin wannan, wanda Ruhun Allah yake cikinsa?”
39 Domin haka Fir'auna ya ce wa Yusufu, “Tun da yake Allah ya nuna maka waɗannan abu duka, ba wani mai basira da hikima kamarka,
40 za ka shugabanci gidana, bisa ga cewarka za a mallaki jama'ata, sai dai da sarauta kaɗai nake gaba da kai.”
41 Fir'auna ya ce wa Yusufu, “Ga shi, na sa ka bisa dukan ƙasar Masar.”
42 Sai Fir'auna ya cire zobensa mai hatimi daga hannunsa ya sa a hannun Yusufu, ya sa masa rigunan lilin masu kyau, ya rataya masa sarƙar zinariya a wuya,
43 ya kuma sa shi ya hau karusarsa ta biyu, suka yi ta shela a gabansa, “Ku ba da hanya.” Ta haka fa ya sa ya zama mai mulki bisa dukan ƙasar Masar.