21 Sai suka ce wa junansu, “A ainihin gaskiya, muna da laifi dangane da ɗan'uwanmu, da yake mun ga wahalar da yake sha, sa'ad da kuma ya roƙe mu mu taimake shi, amma ba mu saurara ba, domin haka wannan wahala ta sauko mana.”
22 Sai Ra'ubainu ya amsa musu, “Ashe, dā ma ban faɗa muku kada ku cuci yaron ba? Amma ba ku saurara ba. To, ga shi fa, ana neman hakkinsa yanzu.
23 Ba su sani ba, ashe, Yusufu yana jinsu, domin akwai tafinta a tsakaninsu.
24 Ya juya waje ɗaya ya yi kuka, sai ya sāke komawa wurinsu ya yi magana da su. Ya ɗauki Saminu daga cikinsu ya ɗaure shi a kan idonsu.
25 Yusufu ya umarta a cika tayakan da hatsi, a kuma mayar wa kowa da kuɗinsa cikin taikinsa, a kuma ba su guzuri don hanya. Haka kuwa aka yi musu.
26 Suka labta wa jakunansu hatsi, suka tashi.
27 Da ɗaya daga cikinsu ya buɗe taikinsa domin ya ba jakinsa tauna a zango, sai ya ga kuɗinsa a bakin taikinsa.