25 Yusufu ya umarta a cika tayakan da hatsi, a kuma mayar wa kowa da kuɗinsa cikin taikinsa, a kuma ba su guzuri don hanya. Haka kuwa aka yi musu.
26 Suka labta wa jakunansu hatsi, suka tashi.
27 Da ɗaya daga cikinsu ya buɗe taikinsa domin ya ba jakinsa tauna a zango, sai ya ga kuɗinsa a bakin taikinsa.
28 Ya ce wa 'yan'uwansa, “An mayar mini da kuɗina, ga shi nan a taiki!”Zuciyarsu ta karai sai suka juya suna duban juna, suna makyarkyata suna cewa, “Me ke nan da Allah ya yi mana?”
29 Sa'ad da suka zo wurin mahaifinsu Yakubu a ƙasar Kan'ana, suka faɗa masa dukan abin da ya same su, suna cewa,
30 “Mutumin, shugaban ƙasar, ya yi mana magana da gautsi, ya ɗauke mu a magewayan ƙasa.
31 Amma muka ce masa, ‘Mu amintattu ne, mu ba magewaya ba ne.