31 Sa'an nan ya wanke fuskarsa, ya fito ya ɗaure, ya umarta a kawo abinci.
32 Aka hidimta masa shi kaɗai, su kuma su kaɗai, domin Masarawa ba sukan ci abinci tare da Ibraniyawa ba, gama wannan abin ƙyama ne ga Masarawa.
33 Aka zaunar da 'yan'uwan Yusufu a gaban Yusufu bisa ga shekarunsu na haihuwa, daga babba zuwa ƙarami. 'Yan'uwan kuwa suka duddubi juna suna mamaki.
34 Daga teburin da yake a gabansa aka riƙa ɗibar rabonsu ana kai musu, amma rabon Biliyaminu ya yi biyar ɗin na kowannensu. Suka kuwa sha, suka yi murna tare da shi.