9 Na ɗauki lamuninsa, a hannuna za ka neme shi. Idan ban komo maka da shi, in kawo shi a gabanka ba, bari alhakin ya zauna a kaina har abada,
10 gama da ba don mun yi jinkiri ba, da yanzu, ai, mun yi sawu biyu.”
11 Mahaifinsu, Isra'ila ya ce musu, “In tilas haka zai zama, sai ku yi wannan, ku ɗiba daga cikin zaɓaɓɓu, mafiya kyau na albarkar ƙasar a cikin tayakanku, ku kai wa mutumin tsaraba, da ɗan man shafawa na ƙanshi da 'yar zuma, da kayan yaji, da ƙaro, da tsabar citta, da ɓaure.
12 Ku ɗauki kuɗi riɓi biyu a hannunku, ku kuma ɗauki kuɗin da aka mayar muku a tayakanku, kila kuskure ne aka yi.
13 Ku kuma ɗauki ɗan'uwanku, ku tashi ku sāke komawa wurin mutumin.
14 Allah Maɗaukaki ya ba ku tagomashi a gun mutumin, har da zai sakar muku da ɗaya ɗan'uwan nan naku tare da Biliyaminu kuma. Ni kuwa idan na yi rashi, na rasa ke nan.”
15 Sai mutane suka ɗauki tsarabar, suka kuma ɗauki riɓin kuɗin a hannunsu tare da Biliyaminu. Suka tashi suka gangara zuwa Masar, suka shiga wurin Yusufu.