16 Sa'ad da labari ya kai gidan Fir'auna cewa, “'Yan'uwan Yusufu sun zo,” abin ya yi wa Fir'auna da fādawansa daɗi ƙwarai.
17 Sai Fir'auna ya ce wa Yusufu, “Ka faɗa wa 'yan'uwanka su yi wannan, ‘Ku yi wa dabbobinku laftu ku koma a ƙasar Kan'ana.
18 Ku ɗauko mahaifinku da iyalanku, ku zo wurina, ni kuwa zan ba ku yankin ƙasa mafificiya a Masar, za ku ci moriyar ƙasar.’
19 Ka kuma umarce su ka ce, ‘Ku ɗauki kekunan shanu daga ƙasar Masar domin 'yan ƙanananku da matanku, ku ɗauko mahaifinku, ku zo.
20 Kada ku damu da kayayyakinku, gama abin da yake mafi kyau duka a ƙasar Masar naku ne.’ ”
21 Haka kuwa 'ya'yan Isra'ila suka yi. Yusufu kuma ya ba su kekunan shanu bisa ga umarnin Fir'auna, ya ba su guzuri don hanya.
22 Ga kowane ɗayansu ya ba da rigar ado, amma ga Biliyaminu ya ba da azurfa ɗari uku, da rigunan ado biyar.