13 A yanzu cikin ƙasar duka, ba abinci, gama yunwar ta tsananta ƙwarai, har ƙasar Masar da ƙasar Kan'ana suka matsu saboda yunwar.
14 Yusufu kuwa ya ƙwalƙwale dukan kuɗin da yake akwai a ƙasar Masar da a ƙasar Kan'ana, domin hatsin da suka saya. Yusufu kuma ya kawo kuɗin cikin gidan Fir'auna.
15 Sa'ad da aka kashe kuɗin da yake a Masar duka da na ƙasar Kan'ana, Masarawa duka suka zo wurin Yusufu, suka ce, “Ka ba mu abinci, don me za mu mutu a kan idonka? Gama kuɗinmu sun ƙare.”
16 Yusufu ya amsa, ya ce, “Ku ba da shanunku, ni kuwa zan ba ku abinci a madadin shanunku in kuɗinku sun ƙare.”
17 Saboda haka suka kai wa Yusufu dabbobinsu, sai Yusufu ya ba su abinci madadin dawakai da garkunan awaki da na tumaki, da garkunan shanu da na jakai, ya tallafe su da abinci a madadin dabbobinsu duka a wannan shekara.
18 Sa'ad da wannan shekara ta ƙare, sai suka zo wurinsa a shekara ta biyu, suka ce masa, “Ranka ya daɗe. Ba za mu ɓoye wa shugabanmu ba cewa kuɗinmu duka mun kashe, garkunan dabbobin kuma sun zama naka. Banda jikunanmu da gonakunmu, ba kuwa abin da ya rage mana.
19 Kada ka bar mu mu mutu, ka yi wata dabara! Kada ka bari mu rasa gonakinmu. Ka musaye mu da abinci, mu da gonakunmu. Mu kuwa za mu zama bayin Fir'auna, ka kuma ba mu iri domin mu rayu, kada mu mutu don kuma kada ƙasar ta zama kango.”