8 Fir'auna kuma ya ce wa Yakubu, “Nawa ne shekarun haihuwarka?”
9 Yakubu ya ce wa Fir'auna, “Shekaruna na zaman baƙuncina, shekara ce ɗari da talatin, shekaruna kima ne cike kuma da wahala, ba su kuwa kai yawan shekarun kakannina ba, cikin baƙuncinsu.”
10 Yakubu kuwa ya sa wa Fir'auna albarka, sa'an nan ya fita daga gaban Fir'auna.
11 Sai Yusufu ya zaunar da mahaifinsa da 'yan'uwansa, ya kuwa ba su mahalli a ƙasar Masar, cikin ƙasa mafi kyau a ƙasar Remesse, kamar yadda Fir'auna ya umarta.
12 Yusufu ya bai wa mahaifinsa da 'yan'uwansa da dukan iyalin gidan mahaifinsa abinci, bisa ga yawan 'ya'yansu.
13 A yanzu cikin ƙasar duka, ba abinci, gama yunwar ta tsananta ƙwarai, har ƙasar Masar da ƙasar Kan'ana suka matsu saboda yunwar.
14 Yusufu kuwa ya ƙwalƙwale dukan kuɗin da yake akwai a ƙasar Masar da a ƙasar Kan'ana, domin hatsin da suka saya. Yusufu kuma ya kawo kuɗin cikin gidan Fir'auna.