23 Maharba suka tasar masa ba tausayiSuka fafare shi da kwari da baka.
24 Duk da haka bakunansu sunkakkarye.Damatsansu sun yayyageTa wurin ikon Allah Mai Girma naYakubu,Makiyayi, Dutse na Isra'ila.
25 Ta wurin Allah na mahaifinka wandazai taimake ka,Ta wurin Allah Mai Iko Dukkawanda zai sa maka albarkaAlbarkun ruwan sama daga bisa,Da na zurfafa daga ƙarƙashinƙasa,Da albarkun mama da na mahaifa.
26 Albarkun hatsi da na gariAlbarkun daɗaɗɗun duwatsu,Abubuwan jin daɗi na madawwamantuddai,Allah ya sa su zauna a kan Yusufu,Da a goshin wanda aka raba shi da'yan'uwansa.
27 “Biliyaminu kyarkeci ne mai kisa,Da safe yakan cinye abin da yakaso,Da maraice kuma yakan raba abin daya kamo.”
28 Waɗannan duka su ne kabilan Isra'ila goma sha biyu, wannan kuma shi ne abin da mahaifinsu ya faɗa musu sa'ad da yake sa musu albarka. Ya sa wa kowannensu albarka da irin albarkar da ta cancance shi.
29 Yakubu ya umarce su, ya ce musu, “Ga shi, lokacin mutuwa ya gabato da za a kai ni wurin jama'ata da suka riga ni. Sai ku binne ni tare da kakannina a cikin kogon da yake a saurar Efron Bahitte,