26 Albarkun hatsi da na gariAlbarkun daɗaɗɗun duwatsu,Abubuwan jin daɗi na madawwamantuddai,Allah ya sa su zauna a kan Yusufu,Da a goshin wanda aka raba shi da'yan'uwansa.
27 “Biliyaminu kyarkeci ne mai kisa,Da safe yakan cinye abin da yakaso,Da maraice kuma yakan raba abin daya kamo.”
28 Waɗannan duka su ne kabilan Isra'ila goma sha biyu, wannan kuma shi ne abin da mahaifinsu ya faɗa musu sa'ad da yake sa musu albarka. Ya sa wa kowannensu albarka da irin albarkar da ta cancance shi.
29 Yakubu ya umarce su, ya ce musu, “Ga shi, lokacin mutuwa ya gabato da za a kai ni wurin jama'ata da suka riga ni. Sai ku binne ni tare da kakannina a cikin kogon da yake a saurar Efron Bahitte,
30 a cikin kogon da yake a Makfela, gabashin Mamre, a ƙasar Kan'ana, wanda Ibrahim ya saya duk da saurar, daga wurin Efron Bahitte, ya zama mallakarsa don makabarta.
31 A can aka binne Ibrahim da Saratu matarsa. A can kuma suka binne Ishaku da Rifkatu matarsa. A can kuma na binne Lai'atu.
32 Da saurar da kogon da yake cikinta, an saye su daga Hittiyawa.”